18 Yuli 2017 - 15:41
Ranar Tunawa Da Nelson Mandela  Ta Duniya

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a sakonsa na ranar Nelson Mandela ta duniya yajinjinawa gwgawarmayar da tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu ya yi a tsawon rayuwarsa.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a sakonsa na ranar  Nelson Mandela ta duniya yajinjinawa gwgawarmayar da tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu  ya yi a tsawon rayuwarsa.

Antonia Guteress  ya ci gaba da cewa; Mandela bai taba mika kai saboda wahalhalu ba ko kuma wulakancin da ya fuskanta, ya jagoranci duniya domin kai wa ga ranaku masu haske.

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 18 ga watan Yuli na kowace shekara a matsayin ranar Nelson Mandela ta duniya, domin tunawa da gwagwarmayarsa.